Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, mai wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawan Najeriya, ya shawarci jam’iyyar APC da ta yi amfani da kalamai masu mutuntawa da tausasawa yayin yakin neman zaben 2027.
Sanatan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da BBC, inda ya ce tsadar rayuwa da matsalolin tattalin arziki sun janyo fushin al’ummar Najeriya, don haka bai kamata a yi musu kamfen da kalaman da za su kara fusata su ba.
Kawu Sumaila ya ce ya gabatar wa kwamitin yakin neman sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu, karkashin jagorancin Abdul’aziz Abubakar Yari, wasu shawarwari da suka shafi halin da al’ummar kasar ke ciki.
Ya ce ya kamata ‘yan jam’iyyar su kasance masu gaskiya wajen bayyana matsalolin da kasar ke fuskanta, musamman matsalar tsaro, inda mutane ke rasa rayukansu, wasu kuma ke barin garuruwansu saboda hare-hare da rashin tsaro.
Sanatan ya kuma yi suka kan wasu mambobin kwamitin yakin neman zaben Shugaba Tinubu, yana mai cewa wasu daga cikinsu suna daga cikin wadanda suka taimaka wajen jefa gwamnatin APC cikin matsalolin da ake fuskanta.
Ya ce duk da cewa suna cikin jam’iyya daya, ya kamata kowa ya amince da gaskiyar halin da ake ciki, domin matsalolin da ake fuskanta ba za a magance su da boye gaskiya ba.
Kawu Sumaila ya ce babban aikin kowace gwamnati shi ne tabbatar da tsaron rayuka, mutunci da dukiyoyin al’umma, kafin samar da sauran abubuwan more rayuwa.
Ya ce muddin ‘yan Najeriya ba su ga sauyi a bangaren tsaro da rayuwar yau da kullum ba, ba za su gamsu da kokarin gwamnati ba.
Ya kwatanta shugabanci da aikin likita, inda ya ce likita kan tausaya wa mara lafiya yayin da yake ba shi magani, amma wani lokaci maganin kan janyo masa ciwo kafin ya samu lafiya.
Dangane da zargin ‘yan adawa cewa APC ba ta da abin da za ta yi wa al’umma alkawari a zaben 2027, Sanata Kawu Sumaila ya ce wasu daga cikin jam’iyyun adawar sun taba haifar wa Najeriya matsaloli fiye da abin da ake zargin APC da shi.
Sanatan ya kuma yi kira musamman ga al’ummar Arewacin Najeriya da su daina jiran gwamnati ko jami’an tsaro kadai wajen magance matsalolin yankin, yana mai cewa kowa ya kamata ya bayar da gudummawarsa wajen ceto yankin daga halin da yake ciki.