Cibiyar Yaƙi da Cututtuka ta Najeriya, NCDC, ta ce aƙalla mutane 252 ne suka mutu sakamakon cutar zazzaɓin Lassa a Najeriya tun farkon shekarar 2026.

Hukumar ta ce zuwa yanzu an tabbatar da mutane 1,035 sun kamu da cutar, yayin da aka samu sabbin mutane 14 da aka tabbatar sun kamu tsakanin 10 zuwa 16 ga watan Agusta.

Sabbin waɗanda suka kamu da cutar sun fito ne daga jihohin Ondo, Bauchi, Edo da Benue.

NCDC ta bayyana cewa adadin mace-macen ya sa yawan mutuwar masu fama da cutar ya kai kashi 24.4 cikin 100, wanda ya haura na shekarar 2025, lokacin da adadin ya tsaya a kashi 18.6 cikin 100.

Hukumar ta ce jihohi 23 sun riga sun samu aƙalla mutum ɗaya da aka tabbatar ya kamu da cutar, a ƙananan hukumomi 117.

NCDC ta ce tana ci gaba da sa ido kan cutar tare da ɗaukar matakan dakile yaɗuwarta a sassan ƙasar.