Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta dauki matakin ladabtarwa kan matashin dan wasanta, Raúl Asencio, bayan dan wasan ya shiga cikin wani lamari da ya shafi rayuwarsa a wajen fili.


Rahotanni sun ce Asencio ya fuskanci hukunci bayan an kama shi yana tuka mota cikin maye a Gran Canaria.


Kotun ta yanke masa hukuncin biyan tarar €14,400, tare da hana shi tuka mota na tsawon watanni takwas.


Wannan lamari ya jawo hankalin Real Madrid, wadda ta nuna cewa ’yan wasanta na da alhakin kare mutuncin kungiyar ba kawai yayin da suke filin wasa ba, har ma a rayuwarsu ta yau da kullum.


Matakin na zuwa ne a lokacin da Asencio ke taka muhimmiyar rawa a tawagar farko ta Real Madrid, inda ake kallonsa a matsayin daya daga cikin matasan ’yan wasan da kungiyar ke da kyakkyawan fata a kansu.


A gefe guda, dan wasan ya kuma fuskanci wata shari’a da ta shafi yada wani bidiyon sirri ba tare da izinin wadanda abin ya shafa ba. Sai dai rahotanni sun bayyana cewa an kawo karshen wannan batu bayan an janye korafin da ake yi masa.


Lamarin ya sake haifar da muhawara kan yadda manyan kungiyoyin kwallon kafa ya kamata su rika daukar mataki idan dan wasa ya aikata abin da zai iya tarnata mutuncinsa ko na kungiyar.