Rahotanni daga Najeriya na cewa mazauna garin Kebbe, da ke ƙaramar hukumar Kebbe a jihar Sokoto, na fuskantar barazanar tsaro bayan wasu da ake zargin ɓarayin daji ne sun buƙaci a ba su naira miliyan 40, tare da barazanar kai hari idan ba a biya kuɗin ba.
Majiyoyi daga garin sun ce waɗanda ake zargin ‘yan bindigar daji ne sun fara bai wa mazauna garin wa’adin kwanaki biyar domin su tara kuɗin.
Sai dai bayan mazauna garin sun roƙe su, an ce sun ƙara tsawaita wa’adin biyan kuɗin.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmed Rufai, ya tabbatar da cewa rundunar ta samu rahoton barazanar.
Ya ce sashen yaƙi da garkuwa da mutane na rundunar, wato AKU, ya fara bincike da ɗaukar matakan da suka dace kan lamarin.
DSP Ahmed Rufai ya ƙara da cewa, bisa bayanan da rundunar ta samu, waɗanda ake zargin ɓarayin daji ne sun bai wa mazauna garin wa’adin zuwa ranar Lahadi domin su samar da kuɗin.
Lamarin ya janyo fargaba tsakanin mazauna garin, musamman saboda barazanar yiwuwar kai musu hari idan ba su samu damar biyan kuɗin da aka nema ba.
Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta ce tana ci gaba da bibiyar lamarin tare da ɗaukar matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.