Aƙalla mutum 23 ne suka mutu sakamakon wata annobar da ake zargin cutar mashaƙo ce a jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya.

Hukumomin lafiya sun ce kawo yanzu, an samu mutane 143 da ake zargin sun kamu da cutar a yankunan da annobar ta shafa.

Kwamishinan Lafiya na jihar Filato, Nicholas Baamlong, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ƙara ƙaimi wajen dakile yaɗuwar cutar.

Ya ce an fara wani gagarumin shirin wayar da kan jama’a, tare da amfani da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki domin taimakawa wajen dakile yaɗuwar cutar.

Jami’an lafiya sun kuma ƙarfafa sa ido da matakan gaggawa a yankunan da annobar ta shafa, domin gano waɗanda ake zargin sun kamu da cutar, da kuma gano mutanen da suka yi mu’amala da su, don hana ƙarin yaɗuwar cutar.

Annobar ta janyo fargaba tsakanin mazauna yankunan da abin ya shafa, inda wasu iyalai suka bayyana cewa ƙananan yara na daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu.

Mashaƙo cuta ce mai saurin yaɗuwa wadda ke iya haifar da matsanancin ciwon numfashi da wasu matsalolin lafiya, musamman ga ƙananan yara da ba a yi wa rigakafi ba.

Najeriya ta fuskanci barkewar cutar mashaƙo a lokuta daban-daban cikin 'yan shekarun nan, musamman a tsakanin ƙananan yara da ba su samu cikakken rigakafin da ya dace ba.

Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya, NCDC, da sauran hukumomin lafiya sun yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su tabbatar da cewa yaran sun samu rigakafin mashaƙo bisa tsarin rigakafin ƙasa.

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta bayyana mashaƙo a matsayin cutar da za a iya kare kai daga gare ta ta hanyar rigakafi, tare da jaddada muhimmancin gano cutar da wuri da kuma ɗaukar matakan da suka dace domin dakile yaɗuwarta.

Barkewar cutar a jihar Filato na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke ƙara ƙarfafa matakan yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa, duk da ƙalubalen da suka haɗa da ƙarancin ɗaukar rigakafi da kuma wahalar kai ayyukan kiwon lafiya zuwa wasu al'ummomi.

Hukumomin lafiya sun yi kira ga mazauna yankunan da abin ya shafa da su kai rahoton duk wani mutum da suke zargin yana nuna alamun mashaƙo, tare da neman taimakon jami'an lafiya cikin gaggawa.