Gwamnatin Jihar Borno ta ce an lalata makarantu fiye da 1,400 a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, yayin da aka kashe malamai 2,295, sakamakon rikicin ta’addanci da yankin ya kwashe shekaru yana fama da shi.
Gwamnatin ta kuma ce kimanin yara miliyan uku ne ke buƙatar tallafin gaggawa a fannin ilimi, sakamakon tasirin rikicin da ya shafi yankin.
Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Umar Usman Kadafur, ne ya bayyana hakan yayin da yake wakiltar Gwamna Babagana Umara Zulum a wani taron tattaunawa na ƙasa na kwanaki biyu kan illar rikici ga lafiyar ƙwaƙwalwar yara a Najeriya, wanda aka gudanar a Maiduguri.
Kadafur ya ce alkaluman na nuna irin mummunan tasirin da rikicin da aka shafe tsawon lokaci ana fama da shi ya yi kan yara, musamman dangane da lafiyar ƙwaƙwalwarsu, iliminsu da makomarsu.
Ya ce duk da rage hare-haren ‘yan ta’adda a wasu yankuna, illar rikicin na ci gaba da bayyana a halayyar yara, da yadda suke kallon kansu da kuma yadda suke amincewa da al’ummominsu.
Ya ce yanayin damuwa da tsoro ba ya ƙarewa nan take bayan an dakile hare-hare, domin abubuwan da yara suka fuskanta na iya barin tasiri mai zurfi a ƙwaƙwalwarsu.
Mataimakin gwamnan ya yi gargaɗin cewa idan ba a kula da raunin ƙwaƙwalwa da yara suka samu ba, hakan na iya haifar da matsalolin ɗabi’a da ɗacin rai, har ma da sanya wasu daga cikinsu cikin haɗarin shiga ƙungiyoyin ‘yan ta’adda.
Kadafur ya ce ayyukan soji kaɗai ba za su iya magance dukkan illolin da rikicin ya haifar ba.
Ya jaddada buƙatar ƙara shirye-shiryen kula da lafiyar ƙwaƙwalwa da tallafin zamantakewa, domin taimaka wa yaran da rikici ya shafa su dawo cikin yanayin rayuwa mai kyau.
Ya kuma yi kira da a samar da tsarin ƙasa na kula da lafiyar ƙwaƙwalwar yara da suka fuskanci rikici, tare da ƙara tura ƙwararrun ma’aikatan lafiya zuwa al’ummomin da rikicin ya shafa.
Haka kuma, ya buƙaci ƙarin saka hannun jari a fannin ilimi da ayyukan ci gaban al’umma.
A nasa ɓangaren, wakiliyar Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, kuma Daraktar Harkokin Lafiya ta Hukumar Leken Asiri ta Najeriya, Dr Patience Omokri, ta ce ya kamata a ɗauki matsalolin da yara suka fuskanta sakamakon rikici a matsayin wani muhimmin al’amari da ya shafi tsaron ƙasa.
Ta ce yaran da suka fuskanci rashin tsaro da ayyukan ta’addanci sun gamu da matsaloli da dama, ciki har da rasa iyaye da gidajensu, garkuwa da su da kuma wasu nau’o’in cin zarafi.
A cewar ta, idan ba a samar wa yaran tallafin da ya dace ba, raunin da suka samu na iya shafar zaman lafiyar al’umma a nan gaba.
A halin da ake ciki, wakilin UNICEF, Francis Otuochi, ya ce yara 270,864 a jihohin Borno, Adamawa da Yobe na buƙatar kulawar lafiyar ƙwaƙwalwa da tallafin zamantakewa a ƙarƙashin shirin Majalisar Ɗinkin Duniya na agajin jinƙai na shekarar 2026.
Ya yi kira ga gwamnatoci da su haɗa shirye-shiryen kula da lafiyar ƙwaƙwalwa cikin manufofin kare yara, kiwon lafiya, ilimi da walwalar jama’a.