Fiye da mutane 900 ne suka mutu sakamakon hare-haren Isra’ila a Zirin Gaza tun farkon wannan shekara, duk da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma, a cewar sabbin alkaluman Ma’aikatar Lafiya ta Gaza.
Ma’aikatar, wadda ke karkashin Hamas, ta ce jimillar Falasɗinawan da suka rasa rayukansu a Gaza tun bayan ayyana tsagaita wutar a ranar 10 ga Oktoba, ta haura 1,300, ciki har da yara 301.
Isra’ila da Hamas sun amince da tsagaita wutar ne bayan bangarorin biyu sun karɓi shirin zaman lafiya mai maki 20 da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya gabatar.
Shirin ya tanadi dakatar da dukkan ayyukan soji, ciki har da hare-haren sama da luguden manyan bindigogi.
Sai dai binciken sashen BBC Verify ya gano wasu bidiyoyi da ke nuna illolin hare-haren Isra’ila a wurare daban-daban a Gaza, ciki har da wani gidan shan shayi da ke bakin teku, sansanonin tantunan mutanen da suka rasa matsugunansu, da kuma jerin gwanon jana’iza a tsakiyar Gaza.
Alkaluman sun nuna cewa watannin baya-bayan nan na daga cikin mafi muni, inda aka samu mutuwar sama da mutane 100 a kowane wata tsakanin watan Afrilu da Agusta.
Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta danganta mace-macen kai tsaye da hare-haren sojin Isra’ila, sai dai alkaluman ba sa bambance tsakanin fararen hula da mayaƙa.