Kwamitin da gwamnatin Jihar Kano ta kafa domin gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar wata dalibar makarantar St. Louis, Maimuna Nihal, ya bayyana cewa binciken da aka gudanar bai gano wata hujja da ke nuna cewa makarantar tana da hannu a mutuwar dalibar ba.
Kwamitin ya mika rahotonsa ga Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Umar Faruk Ibrahim, bayan gudanar da cikakken bincike a dakunan kwanan dalibai, asibiti da sauran sassan makarantar.
Da yake gabatar da rahoton, Mataimakin Shugaban Kwamitin kuma Sakataren Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu, Comrade Baba Abubakar Umar, ya ce an binciki yadda dalibar ta fadi ba zato ba tsammani, inda aka sanar da iyayenta cikin gaggawa tare da garzayawa da ita asibiti.
Ya ce likitoci sun tabbatar da cewa mutuwar dalibar ba ta da alaka da wani cin zarafi ko musgunawa.
Kwamitin ya kuma ce bai samu wata hujja da ke nuna cewa an ci zarafin dalibar, an yi mata wani mummunan duka ko kuma an yi mata horo da ya kai ga mutuwarta ba.
A nasa bangaren, Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Umar Faruk Ibrahim, ya jajanta wa iyalan marigayiyar, tare da addu’ar Allah Ya gafarta mata.
Ya kuma yabawa kwamitin bisa gudanar da binciken cikin gaskiya da adalci, yana mai cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da daukar matakan kare lafiya da rayukan dalibai a fadin jihar.