Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da wani kwamiti na musamman domin daukar matakan gaggawa kan barkewar cutar Mashako a jihar.


An kafa kwamitin ne da nufin karfafa matakan dakile cutar, inganta martanin hukumomin lafiya da kuma hana ci gaba da yaduwar cutar a tsakanin al’ummomin jihar.


Kwamitin zai mayar da hankali wajen daidaita kokarin hukumomin lafiya da sauran masu ruwa da tsaki, tare da kara wayar da kan jama’a kan hanyoyin kariya daga cutar.


Haka kuma, za a karfafa matakan sa ido da daukar matakin gaggawa a wuraren da aka samu rahoton bullar cutar, domin rage barazanar da cutar ke iya haifarwa ga al’umma.


Gwamnatin ta bayyana kafa kwamitin a matsayin wani mataki na kara karfafa yaki da cutar da kuma kare lafiyar al’ummar Jihar Kano.