Akalla mutane 60 ne suka mutu sakamakon sabuwar arangama tsakanin dakarun gwamnatin Yemen da ke samun goyon bayan Saudiyya da mayaƙan Houthi, kamar yadda majiyoyin lafiya da na soji suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Rahoton ya ce an shafe sa’o’i ana gwabza faɗa a wani yanki da ke kudu maso yammacin Yemen, inda aka kashe sojojin gwamnati 26.
A gefe guda kuma, majiyoyin lafiya da na soji na ƙungiyar Houthi, wadda Iran ke goyon baya, sun ce mayaƙansu 31 ne aka kashe a arangamar.
Har ila yau, fararen hula na cikin waɗanda suka mutu, bayan da wani hari da makami mai linzami ya afkawa wata motar bas a birnin Taiz.
Wata majiya daga ɓangaren lafiya ta ce harin ya kashe fararen hula shida, tare da raunata wasu bakwai.
Ƙungiyar Houthi, wadda ke kiran kanta Ansar Allah, tana iko da wani babban yanki na arewacin Yemen da kuma sassan gabar tekun Bahar Maliya, ciki har da babban birnin ƙasar, Sanaa.
A daya bangaren kuma, Kwamitin Shugabancin Yemen, wanda ƙasashen duniya suka amince da shi a matsayin gwamnatin ƙasar, na samun goyon bayan Saudiyya.
Gwamnatin tana iko da mafi yawan gabashin Yemen da kuma gabar tekun kudancin ƙasar, ciki har da tashar jiragen ruwa ta Aden.