Fadar gwamnatin Rasha, Kremlin, ta ce Shugaba Vladimir Putin ya bayar da umarnin dakatar da hare-haren da ake kai wa Kyiv na tsawon kwanaki uku, a daidai lokacin da wakilan Shugaban Amurka Donald Trump ke shirin ziyartar Ukraine domin tattauna hanyoyin kawo ƙarshen yaƙin.
Wakilan na Amurka, Steve Witkoff da Jared Kushner, sun isa Moscow, inda ake sa ran za su gana da Shugaba Putin kafin su zarce zuwa Kyiv domin ganawa da Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky. Wannan ne karon farko da Witkoff da Kushner za su kai irin wannan ziyara a Ukraine.
Shugaba Trump ya ce wakilan na ɗauke da wata sabuwar shawara da nufin kawo ƙarshen yaƙin, sai dai bai bayyana cikakken bayanin shirin ba.
A cewar Kremlin, dakatar da hare-haren na kwanaki uku na da nasaba da ƙoƙarin samar da yanayi mai kyau domin tattaunawar diflomasiyya.
A wani ci gaba makamancin haka, Shugaba Zelensky ya ce Ukraine ma za ta dakatar da hare-haren sama kan Moscow yayin ziyarar wakilan Amurka, domin bai wa ƙoƙarin sulhu damar samun nasara.
Sai dai matakin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da gwabza yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine, wanda ya shiga shekara ta biyar, tare da ƙaruwa a hare-haren jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami a bangarorin biyu.