Gwamnatin Nijar ta zargi Faransa a hukumance da goyon bayan wani yunƙurin hargitsa ƙasar da ta ce ya faru a ranakun 28 da 29 ga watan Agusta.

A cikin wata sanarwa, gwamnatin ta ce arangamar da ta faru a sansanin sojin sama na 101 da ke Yamai tana da alaƙa da ƙasashen waje.

Ta ce tana da “ƙwararan shaidu masu yawa” da suka shafi harin, kuma tana nazarin yiwuwar shigar da ƙara a gaban kotunan ƙasa da ƙasa.

Gwamnatin Nijar ta kuma zargi Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, da jagorantar wata ƙungiya ta mutane da hukumomi da ke goyon bayan yunƙurin, tare da zargin cewa wasu ƙasashen Afirka da ba ta bayyana sunayensu ba sun taka rawa a lamarin.

Sai dai kawo yanzu, gwamnatin Nijar ba ta gabatar da hujjoji a bainar jama'a da za su tabbatar da waɗannan zarge-zargen ba.

Sansanin sojin sama na 101, wanda aka kai wa hari a ranar 29 ga Agusta, yana cikin rukunin filin jirgin saman Diori Hamani da ke Yamai. A sansanin ne ake ajiye wasu jiragen yaƙi da jirage marasa matuƙa na sojin Nijar, da kuma rundunar haɗin gwiwa da ke yaƙi da ta’addanci a yankin Sahel.

Rahotanni sun ce sojojin Rasha da Italiya ma suna da sansani a wannan yankin.

Gwamnatin Nijar ta ce baya ga Rasha, ta kuma samu taimakon Aljeriya wajen tunkarar lamarin.

Rasha ta tabbatar da cewa dakarunta sun taimaka wa sojojin Nijar wajen dakile abin da aka bayyana a matsayin yunƙurin juyin mulki da aka kai ranar Asabar.