Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da amincewa da yarjejeniyar sayar wa Saudiyya makamai da kayan aikin soji da darajarsu ta kai dala biliyan biyar.

A cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce Saudiyya ta nemi sayen dubban bama-bamai, da na’urorin jagorantar makamai masu linzami masu dogon zango.

Ta ce yarjejeniyar ta kuma ƙunshi manyan makamai da kayayyakin gyara, sinadarai, da kuma ayyukan tallafin fasaha, dabarun sufuri da samar da kayayyakin da suka shafi makaman.

A cewar Amurka, yarjejeniyar na daga cikin matakan ƙarfafa tsaron Saudiyya, wadda take ɗaya daga cikin ƙawayenta masu muhimmanci a yankin.

Ma’aikatar ta ce yarjejeniyar za ta kuma taimaka wajen inganta zaman lafiyar siyasa da ci gaban tattalin arziki a yankin Tekun Fasha.

Ta ƙara da cewa sayar da makaman zai taimaka wajen ƙarfafa ƙarfin tsaron sararin samaniyar Saudiyya da kuma ba ta damar fuskantar barazanar tsaro da ake samu a yankin a halin yanzu.