Hedikwatar tsaron kasarnan ta ce dakarunta sun ceto mutane 36 da aka yi garkuwa da su tare da hallaka ’yanta’adda da dama a sabbin ayyukan soji da suka gudanar a sassa daban-daban na ƙasar.
Daraktan Ayyukan Yaɗa Labaran Sojoji, Manjo Janar Michael Onoja ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, kan ayyukan sojin da aka gudanar tsakanin 31 ga Agusta zuwa 3 ga Satumban, 2026.
Ya ce dakarun sun hallaka wani ɗanta’adda a ranar 1 ga Satumba, bayan da suka tarwatsa wani abin fashewa da aka dasa a kan babbar hanyar samar da kayayyaki ta Miyanti-Banki Junction a Bama, Jihar Borno.
A cewarsa, dakarun sun kwato bindiga, harsasai da kuma na’urar tayar da bam bayan wannan samamen.
Ya ce an kuma hallaka wani ɗanta’adda yayin wata arangama da aka yi a Lamusuri Crossing Point da ke Gujba, Jihar Yobe, inda aka kwato bindiga da harsasai.
Onoja ya ce dakarun sun kuma kama wani ɗanta’adda da ya tsere daga hannun ƙungiyar a kusa da Sabsawa, Bama, a ranar 31 ga Agusta, bayan ya tsere saboda yunwa da tsananin wahala.
Ya ce dakarun sun kama wani mutum a Konduga da ake zargi da safarar kayan abinci zuwa wani sansanin ’yanta’adda a Bama.
A cewarsa, dakarun sun kuma kama wani tsohon ɗanta’adda da ya koma mai ba da bayanan sirri a Damasak, Ƙaramar hukumar Mobbar, a ranar 1 ga Satumba.
Onoja ya ce mata da yara 21 sun miƙa wuya ga dakarun a Mafa da ke Dikwa, a ranar 2 ga Satumba, bayan ɓarkewar faɗa tsakanin ƙungiyoyin ’yanta’adda masu hamayya da juna.
Ya ƙara da cewa an kuma kama wani ɗanta’adda da ya tsere a kusa da gadar Amuda da ke Gwoza, yayin da aka kama wani da ake zargi ɗan leƙen asirin ’yanta’adda ne a kan hanyar Kauwa zuwa Kukawa.
Onoja ya ce dakarun Operation Fansan Yamma sun ci gaba da kai hare-haren soji kan ’yanta’adda da masu garkuwa da mutane a jihohin Kaduna, Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara.
Ya ce dakarun sun halaka wasu manyan kwamandojin ’yanta’adda guda biyu tare da jikkata wani na uku yayin wani samame da suka kai kan wasu maɓoyar ’yanta’adda da ake zargi a Kogo da ke Matazu, Jihar Katsina, a ranar 31 ga Agusta