Hukumar dakile cutuka masu yaɗuwa ta Najeriya NCDC ta fitar da wata sanarwar gargaɗi game da yaɗuwar cutar mashaƙo ta Diphtheria a ƙasar, inda ta bayyana damuwa kan yadda cutar ke ci gaba da barazana ga lafiyar al'umma.
Babban abin da ya fi tayar da hankali a cikin rahoton shi ne cewa, kusan kashi 68 cikin 100 na mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar ba su taɓa karɓar allurar rigakafi ba. Wannan babban gibi na rashin rigakafi yana nuna yadda cutar ke samun ƙofar shiga cikin sauƙi tsakanin al'ummomin da ba su da kariya.
Hukumomi sun jaddada cewa rashin yin rigakafin shi ne babban makamin da ke rura wutar yaɗuwar cutar.
Binciken na NCDC ya nuna cewa jihohi takwas kacal a faɗin Najeriya ne ke ɗauke da kashi 98 cikin 100 na dukkanin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar.
Wannan kididdigar tana nuna cewa cutar ta mamaye waɗannan yankuna da ke buƙatar tallafin gaggawa na kiwon lafiya.