Kungiyar ’Yan Jaridu ta Kasa (NUJ), reshen Jihar Kano, ta yi tir da harin da aka kai wa ’yan jarida da ke aikin dauko rahoton taron jam’iyyar APC a Filin Wasa na Sani Abacha da ke Kano a ranar Asabar.
Kungiyar ta bayyana harin, wanda ake zargin wasu ’yan daba ne suka kai wa ’yan jarida tare da lalata motar gidan rediyon kasa, Pyramid FM Kano, a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, tare da cewa barazana ce ga ’yancin aikin jarida.
A cikin wata sanarwa da Shugaban NUJ na Jihar Kano, Comrade Suleiman Abdullahi Dederi, da Sakatarenta, Comrade Hauwa Suleiman Zahradeen, suka sanya wa hannu, kungiyar ta ce ta damu matuka da harin, musamman ganin yadda ya faru a wani taron siyasa gabanin zaben 2027.
NUJ ta jaddada cewa bai kamata a kai wa manema labarai hari, tsoratarwa ko tsangwama yayin da suke gudanar da halastaccen aikinsu ba.
Kungiyar ta ce kai hari ga ’yan jaridar da ke ruwaito lamuran siyasa ba kai hari ga kafafen yada labarai kadai ba ne, illa koma baya ne ga dimokuradiyya, domin kafafen yada labarai masu zaman kansu na taka muhimmiyar rawa wajen fadakar da jama’a da kuma tabbatar da dimokuradiyya.
Ta kuma bayyana cewa ’yan jarida na daga cikin muhimman masu ruwa da tsaki a kowace al’umma, domin aikinsu shi ne sanar da jama’a, samar da dandalin bayyana ra’ayoyi daban-daban da kuma ruwaito harkokin siyasa ba tare da nuna son kai ba.
Kungiyar ta ce ta damu matuka game da tsaron ’yan jaridun da ke ruwaito ayyukan siyasa, musamman a lokacin manyan taruka inda suke fuskantar barazana.
NUJ ta ce maharan sun yi amfani da adda da wuka wajen lalata motar Radio Nigeria Pyramid FM, duk da kasancewar jami’an tsaro a cikinta, lamarin da ta ce ya kara nuna bukatar daukar matakin gaggawa.
Kungiyar ta jajantawa shugabannin gudanarwa da ma’aikatan Radio Nigeria Pyramid FM Kano kan harin da barnar da aka yi wa motarsu, tare da jajantawa ’yan jarida da sauran mutanen da ke cikin motar.
Duk da yaba wa jami’an tsaro kan kokarinsu na tabbatar da zaman lafiya a tarukan jama’a, NUJ ta bukaci a gudanar da cikakken bincike domin gano tare da kama wadanda suka aikata harin, sannan a gurfanar da duk wanda aka samu da laifi domin ya fuskanci hukunci bisa doka.