Ƙungiyar Malaman Makarantu ta Ƙasa NUT reshen Karamar Hukumar Rogo a nan Kano ta ƙaddamar da shirin koyar da malamai 400 aikin sanyawa, kulawa da gyaran na’urorin lantarki na Solar.
Wannan na cikin sanarwar da Jami’in Yaɗa Labarai na Karamar Hukumar Rogo, Abdu Bako Abdullahi, ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa, Shugaban NUT na Karamar Hukumar Rogo, Malam Aliyu Suleiman, ya ce shirin zai bai wa malaman ƙarin ƙwarewar sana’a da za ta taimaka musu wajen samun abin dogaro da kai.
Malam Aliyu Suleiman ya ce malamai 400 za su amfana da shirin, inda za a koya musu yadda ake sanya na’urorin Solar, kula da su da kuma gyara su.
Ya buƙaci malaman da za su halarci horon su mayar da hankali domin samun ƙwarewar da za ta amfani kansu da al’umma.