Masu ababen hawa da ke bin titin Onitsha zuwa Owerri a Jihar Anambra sun koka kan yadda jami’an Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Anambra ke ci gaba da muzanta musu tare da kakaba musu tarar da suka ce ba ta dace ba, musamman a wuraren da titin ya lalace kusa da tashar People’s Club.

Wasu daga cikin direbobin da suka zanta da jaridar Punch sun zargi jami’an hukumar da amfani da lalacewar titin wajen karbar kudade daga hannun masu ababen hawa. 

Sun ce ana karbar kudade tsakanin dubu N150 zuwa dubu N300 daga masu motoci na kashin kansu da direbobin tasi da na motocin haya da ke bin wannan hanya