Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya amince da baiwa dukan ma'aikatan Kano na kananan hukumomi 44 dake mataki na 1 zuwa mataki na 14 a aiki kyautar naira dubu ashirin, don basu damar gudanar da bukukuwan sallah cikin walwala da iyalansu. 


Wannan na zuwa ne Jim kadan bayan da Gwamnatin ta biyan albashin ma'aikata na wannan watan na mayu. 


Sanarwar hakan na kunshe ne cikin wata takarda da aka rabawa manema Labarai, Mai dauke da sa hannun Musa Tanko Muhammad, jami'in yada labarai a ofishin Sakataren Gwamnatin kano