Babban jami'in manufofin kasashen waje na kungiyar, Kaja Kallas, shi ne ya bayyana haka bayan taron ministocin harkokin wajen ƙungiyar da aka yi a ƙasar Cyprus.


Kallas ya ce ƙasashen Turai ba za su iya zama a tsaka-tsaki ba saboda sun riga sun zaɓi ɓangare guda, wato suna goyon bayan Ukraine ɗari bisa ɗari.


EU ta bayyana cewa ƙoƙarinta ba zai maye gurbin rawar da Amurka ke takawa ba a shirin samar da zaman lafiya tsakanin ƙasashen biyu ba.




Maimakon sulhu, EU na shirin ci gaba da amfani da ƙarfinta wajen sanya sabbin takunkumai don tilasta wa Rasha amincewa da ƙudurorin zaman lafiya.


Wannan jawabi ya kawo ƙarshen jita-jitar da ake ta yi na cewa ƙungiyar na shirin naɗa wani babban jami'i kamar tsohuwar shugabar Jamus Angela Merkel ko Mario Draghi domin ya jagoranci tattaunawa da gwamnatin Moscow.


A gefe guda, fadar Kremlin ita ma ta daɗe da bayyana cewa ba za ta amince da EU a matsayin mai shiga tsakani ba, tana mai zargin ƙungiyar da kasancewa mamba kai-tsaye a yaƙin, ta hanyar bai wa Ukraine makamai da kuɗaɗe.