Jose Mourinho ya amince da kwantiragin shekara uku domin komawa matsayin kocin Real Madrid, sai dai ba za a gabatar da shi a hukumance ba har sai bayan zaɓen shugaban ƙungiyar da za a gudanar a ranar 7 ga watan Yuni.
Rahotanni sun nuna cewa kwantiragin Mourinho zai fara aiki ne kawai idan shugaban ƙungiyar na yanzu, Florentino Perez, ya sake samun nasara a zaɓen.
Perez ya sanar da gudanar da sabon zaɓen ne a wani taron manema labarai da aka yi a farkon watan nan, inda ya zargi wasu kafafen yaɗa labarai da kuma hukumar La Liga da gudanar da abin da ya kira “yaƙin tsari” a kansa.
Perez mai shekara 79 ya kasance shugaban Real Madrid tun daga shekarar 2009, bayan ya taba rike mukamin tsakanin 2000 da 2006. Sai dai ƙungiyar ta shafe kakar wasa biyu a jere ba tare da lashe wani babban kofi ba.
Attajiri Enrique Riquelme ne ke ƙalubalantar Perez a zaɓen shugaban ƙungiyar, wanda shi ne karo na farko cikin kusan shekaru 20 da aka samu hamayya mai ƙarfi a zaɓen. Duk da haka, ana hasashen Perez zai sake lashe zaɓen.
Mourinho ya bar aikinsa na horar da Benfica bayan ya karɓi ragamar ƙungiyar a watan Satumba, inda ya jagorance ta zuwa matsayi na uku a gasar Primeira Liga ta Portugal.
A wa’adinsa na farko a Real Madrid daga 2010 zuwa 2013, Mourinho ya lashe kofin La Liga, Copa del Rey da kuma Spanish Super Cup.
Idan komawarsa ta tabbata, zai maye gurbin Alvaro Arbeloa, wanda aka naɗa a watan Janairu bayan tafiyar Xabi Alonso.
Real Madrid ta kammala kakar 2025/26 ba tare da lashe kofi ba, yayin da FC Barcelona ta lashe gasar La Liga bayan nasarar da ta samu a wasan El Clasico.
Haka kuma ƙungiyar ta yi bankwana da gasar Champions League bayan Bayern Munich ta fitar da ita da jimillar ƙwallaye 6-4 a matakin kwata-fainal.
Bayan barinsa Real Madrid a 2013, Mourinho ya sake komawa Chelsea inda ya lashe Premier League da EFL Cup a kakar 2014/15. Daga nan ya horar da Manchester United, inda ya lashe Europa League, EFL Cup da Community Shield kafin a sallame shi a 2018.
Daga baya ya jagoranci Tottenham Hotspur, Roma — inda ya lashe UEFA Europa Conference League a 2022 — da kuma Fenerbahce kafin ya koma Benfica.