Gwamnatin Faransa ta sanar a ranar Litinin cewa ta tare wani jirgin dakon mai da ake zargin yana da alaka da Rasha a Tekun Atlantika, a wani sabon mataki na yaki da jiragen da ake zargin suna taimakawa Moscow wajen kauce wa takunkuman kasashen yamma.
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya bayyana cewa an kama jirgin mai suna Tagor a safiyar Lahadi a ruwan kasa da kasa tare da hadin gwiwar Birtaniya da wasu abokan hulda.
Mahukuntan Faransa sun ce jirgin ya taso ne daga birnin Murmansk da ke arewa maso yammacin Rasha, kuma yana kan hanyarsa ta zuwa garin Limbe da ke kasar Kamaru lokacin da aka tare shi.
A cewar jami’an kula da harkokin teku na Faransa, jirgin na amfani da tutar Kamaru ba bisa ka’ida ba, lamarin da ya haifar da shakku kan sahihancin rajistarsa.
Macron ya ce ba za a amince da duk wani yunkuri na karya dokokin kasa da kasa ko kauce wa takunkuman da aka kakaba wa Rasha ba.
Ya kara da cewa irin wadannan jirage na barazana ga muhalli da kuma lafiyar masu amfani da hanyoyin ruwa saboda rashin bin ka’idojin zirga-zirgar jiragen ruwa.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an rundunar ruwa ta Faransa sun aiwatar da samamen ne fiye da mil 400 na teku daga gabar Brittany, inda suka sauka a jirgin daga sama ta hanyar jirgin sama mai saukar ungulu.
Binciken takardun jirgin ya tabbatar da cewa akwai matsaloli game da tutar da yake amfani da ita, wanda ya sa aka yanke shawarar rakashi zuwa wani wurin ajiye jiragen ruwa domin ci gaba da bincike.
Jirgin yana dauke da ma’aikata 23, kuma an bayyana cewa kusan babu mai a cikinsa lokacin da aka kama shi.
Jami’in kula da harkokin teku na yankin Atlantika, Guillaume Le Rasle, ya ce jirgin na cikin jerin jiragen da Tarayyar Turai da Amurka suka kakaba wa takunkumi.
Ya bayyana cewa hukumomi sun dade suna bibiyar jirgin, kuma an dauki matakin karkatar da shi ne domin tabbatar da sahihancin tutarsa da sauran takardunsa.
Rahotanni sun nuna cewa jirgin ya kan sauya tutocin kasashe daban-daban akai-akai domin kauce wa sa ido da kuma takunkumi, wata dabara da ake kira "flag-hopping."
Tun daga watan Satumban shekarar da ta gabata, Faransa ta tare wasu jirage uku da ake zargin suna cikin abin da ake kira “shadow fleet” na Rasha, wato jiragen da ake amfani da su wajen safarar mai da sauran kayayyaki ba tare da bin takunkuman kasa da kasa ba.
Kasashen yamma sun kakaba wa daruruwan jiragen ruwa masu alaka da Rasha takunkumi tun bayan mamayar Ukraine da Rasha ta fara a shekarar 2022.
A halin yanzu, kusan jiragen ruwa 600 da ake zargin suna cikin wannan “shadow fleet” na Rasha suna fuskantar takunkumin Tarayyar Turai.
Sai dai Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya sha sukar irin wadannan kamun jiragen ruwa, yana mai bayyana su a matsayin "fashin teku" da ake yi da sunan dokokin kasa da kasa.