Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan jami’an ‘yan sanda a hanyar Amansea–Ndiora–Ndiukwuenu–Awa–Ufuma da ke karamar hukumar Orumba South a jihar Anambra, inda suka kashe jami’an ‘yan sanda biyu nan take.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a daren Lahadi yayin da jami’an ke dawowa daga wani aiki da suka je gudanarwa.

A cewar shaidu, maharan sun fake a cikin daji da ke kusa da hanyar, inda suka bude wa jami’an wuta da zarar sun iso yankin. Harbin bindigar ya jefa mazauna yankunan da ke kusa cikin tsoro da firgici.

Wani direban adaidaita sahu da ke amfani da hanyar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce yana dawowa daga Ezira lokacin da ya ji karar harbe-harbe.

Ya ce:

“Lamarin ya faru ne a daren jiya. Ina cikin tafiya sai na ji karar harbin bindiga. Nan take na juya baya domin neman mafaka.
Bayan harbin ya lafa, na ci gaba da tafiyata. Da na isa wurin, sai na ga jami’an ‘yan sanda biyu kwance a kasa ba su da rai a gefen motarsu ta sintiri.”

Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna gawarwakin jami’an biyu kwance a gefen motar sintiri cikin jini, yayin da mai daukar bidiyon ke kira ga hukumomi da su dauki mataki.

Da aka tuntubi Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Anambra, CP Ikioye Orutugu, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce jami’an ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike tun daga daren Lahadi kuma sun kara kaimi wajen farautar wadanda suka kai harin.

A cewarsa:

“Wasu jami’an ‘yan sanda suna dawowa daga wani aiki ne lokacin da wasu mahara suka yi musu kwanton bauna tare da bude musu wuta. A sakamakon haka mun rasa jami’ai biyu.”

Kwamishinan ya kara da cewa zai kai ziyara wurin da harin ya faru domin duba halin da ake ciki tare da tsara karin matakan tsaro domin hana sake aukuwar irin wannan hari a jihar.

Ya kuma gargadi direbobi da sauran jama’a da su yi taka-tsantsan yayin da suke tafiya a kan hanyoyi, musamman idan suka ci karo da wuraren bincike da ba su da motocin ‘yan sanda ko kuma jami’an tsaro da aka san su a hukumance.

Ya bukaci jama’a da su sanar da ofishin ‘yan sanda mafi kusa idan suka ga wani wurin bincike da ke da alamun shakku, domin tabbatar da tsaro da kare rayuka.