Farashin Fetur Ya Tashi da Kashi 643% Cikin Shekaru Uku a Mulkin Tinubu — Rahoto

Farashin man fetur a Nijeriya ya ƙaru da kashi 643 cikin 100 tsakanin watan Mayun 2023 da Mayun 2026, inda ya tashi daga N175 zuwa kusan N1,300 kan kowace lita, kamar yadda wani rahoto da jaridar The PUNCH ta wallafa ya nuna.

Rahoton ya danganta hauhawar farashin da matakin cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar jim kaɗan bayan rantsar da shi a ranar 29 ga Mayun 2023, da kuma sauye-sauyen manufofin musayar kuɗaɗen waje da gwamnatin ta aiwatar.

Bayan shekaru uku, ana sayar da litar man fetur tsakanin N1,300 zuwa N1,400 a sassa daban-daban na ƙasar, idan aka kwatanta da kusan N800 da ake sayar da ita a watannin baya.

Rahoton ya ce sabon tashin farashin ya samo asali ne daga rikicin da ke ci gaba da ƙamari a Gabas ta Tsakiya, wanda ya haddasa tangarɗa a harkar samar da mai a duniya, tare da matsalolin da suka shafi zirga-zirgar jiragen ruwa ta Mashigar Hormuz.

A ranar rantsuwarsa, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa “tallafin mai ya tafi,” lamarin da ya haifar da tashin farashin fetur daga tsakanin N175 da N200 zuwa sama da N500 kan kowace lita a wancan lokaci.

Kamfanin NNPC, wanda shi ne babban mai shigo da man fetur a lokacin, ya fara aiwatar da sabon tsarin farashin ta hanyar ƙara farashin man a gidajen mai nasa.