Mawakin ya ce da ace shi aka ba irin wannan kujera, da ya gindaya sharudda ga Shugaban Kasa kafin ya karba, kuma da zai yi murabus idan har bai iya kawo canji mai anfani cikin shekaru uku ba. Ya ce:


“Duk inda ba zan iya kawo sauyi mai anfani ba, bana son kasancewa a wurin. Bata lokaci ne kawai.”


Soja Boy ya kuma yi zargin cewa babban abin da shugaban Hukumar Fina-finai ta Nijeriya ke yi shi ne halartar tarukan Kannywood a kasashen waje kamar India, Paris, London da Jamus ta hanyar takardun izinin gwamnati (memos), yana daukar hotuna yana wallafawa a shafukansa.


Ya yi kira ga masana’antar kirkire-kirkire ta Arewa da su “zabi shugabanninsu,” yana mai cewa shugabanni dole ne su tsaya tsayin daka wajen kare muradun masana’antarsu.


Har zuwa yanzu, Ali Nuhu bai fito fili ya mayar da martani kan wannan bidiyo ba. Duk da haka, wadannan kalamai zarge-zarge ne na Soja Boy kawai, kuma ba a tabbatar da sahihancinsu ta wata hanya mai zaman kanta ba.