Gwamnatin Tarayya ta yi ga kamfanionin Samar da siminti a Najeriya da su rage farashin siminti domin saukaka manyan aiyukan gine gine a kasarnan.


Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a wajen ƙaddamar da sabon tambarin kamfanin Lafarge Africa, wanda yanzu aka sake masa suna zuwa HBM bayan kamfanin HUAXIN Group na ƙasar Sin ya mallake shi.


Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman ga Ministan kan Harkokin Yaɗa Labarai, Francis Nwaze, ya fitar a ranar Litinin.


Da yake jawabi a gaban shugabannin masana’antu, masu zuba jari da sauran masu ruwa da tsaki a Otal ɗin Lagos Continental da ke Legas, Umahi ya ce gwamnatin tarayya za ta fara tattaunawa a hukumance da kamfanonin samar siminti daga ranar 1 ga Yuli domin magance abin da ya bayyana a matsayin matsalar da ta daɗe tana ci wa Yan Najeriya tuwona kwarya, na tsadar farashin siminti.



Ministan ya jaddada cewa wajibi ne kamfanonin samar siminti su ɗauki alhakin rage farashin kayayyakinsu maimakon su riƙa sa ran gwamnati za ta ci gaba da sauya sharuddan kwangilolin ayyuka saboda tashin farashin kayan gini.