Magoya bayan mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore, sun zargi jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da kama shi da ƙarfi a ranar Litinin duk da umarnin kotu da ya tanadi a tsare shi a gidan gyaran hali.
Zargin ya biyo bayan umarnin da Mai Shari’a Mohammed Umar ya bayar na a tsare Sowore a Gidan Gyaran Hali na Kuje har sai an yanke hukunci kan buƙatarsa ta neman dakatar da aiwatar da wani umarni na baya da ya soke belinsa.
Mai shari’ar ya kuma yi watsi da buƙatar da Sowore ya gabatar na ya janye daga sauraron shari’ar bisa zargin nuna son kai, sannan ya ɗage sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Yuni domin sauraron buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin.
Bayan kammala zaman kotun, magoya bayan Sowore sun yi zargin cewa jami’an DSS sun yi amfani da ƙarfi wajen cafke shi a harabar kotun, suna ƙoƙarin tafiya da shi tare da jikkata shi a yayin da lamarin ke faruwa.