Cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar sun bayyana cewa "Muna sanar da jama’a cewa fim din Kaddara da daukacin masu shirya fim din ba su da wata alaka da kalaman da Nafisa Abdullahi tayi kan batun aure" 


Inda suka Kara da cewa, Ra’ayin da ta bayyana ra’ayinta ne na kashin kanta, kuma ba ya wakiltar manufar fim din Kaddara, masu shirya shi, ko duk wani bangare da ke da alaka da aikin.


Sanarwar ta cigaba da bayyana cewa " Mu a matsayinmu na masu shirya fina-finai, muna mutunta darajar aure da muhimmancinsa a cikin addini da al’adunmu" . Haka kuma muna Allah wadai da duk wani furuci da zai iya rage martabar aure ko ya jawo rudani a tsakanin al’umma.


A karshe kamfanin na Abnur Entertainment ya roki masoya da masu kallon fim din Kaddara da su bambanta tsakanin ra’ayin mutum da kuma manufar aikin da ake gabatarwa. Fim din Kaddara aiki ne na nishadantarwa da fadakarwa, kuma ba shi da wata alaka da wannan batu.