Yayin da farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya koma matakin da yake kafin rikicin da ya ɓarke tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran, har yanzu masu amfani da man fetur a Najeriya ba su ga wani gagarumin sauyi a farashin man a gidajen mai ba.

Farashin ɗanyen mai nau’in Brent ya faɗi sosai bayan samun sauƙin rikicin Gabas ta Tsakiya da kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin da ke rikici. Tun da farko, tashin hankalin ya haddasa fargaba a kasuwannin duniya, musamman saboda barazanar rufe mashigin Hormuz, wata muhimmiyar hanyar jigilar mai da kusan kashi ɗaya bisa biyar na man da ake amfani da shi a duniya ke bi ta cikinta.

Duk da koma bayan farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya, raguwar da aka samu a farashin fetur a Najeriya ba ta wuce naira 75 ba a wasu wurare, lamarin da ya sa jama’a da dama ke ci gaba da kokawa.

Rahotanni sun nuna cewa a wasu yankunan Arewacin Najeriya, har yanzu ana sayar da litar fetur kan fiye da naira 1,000, duk da raguwar farashin ɗanyen mai a duniya.

Wasu daga cikin 'yan Najeriya sun bayyana damuwarsu kan yadda raguwar farashin mai a kasuwannin duniya ba ta bayyana sosai a cikin farashin da suke biya a gidajen mai, suna masu fatan ganin ƙarin sauƙi a nan gaba.