Ofishin Jakadancin ƙasar Ireland da ke Najeriya ya sanar da cewa za a fara karɓar buƙatun shiga Shirin Ireland Fellows Programme na shekarar 2026 daga ranar 29 ga Yuni, inda zai bai wa 'yan Najeriya damar yin karatun digiri na biyu (Master's) a ƙasar Ireland tare da cikakken tallafin karatu.


Ofishin jakadancin ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma'a, yana mai cewa shirin a buɗe yake ga ƙwararrun ma'aikata masu tasowa da kuma masu matsakaicin gogewa daga Najeriya da Ghana, waɗanda ke son yin karatun digiri na biyu na tsawon shekara guda a manyan jami'o'in ƙasar Ireland.


Sanarwar ta ce, Za a buɗe karɓar buƙatun shiga Shirin Ireland Fellows Programme daga ranar 29 ga Yunin 2026! Ku nemi wannan dama ta yin karatun digiri na biyu a ƙasar Ireland tare da cikakken tallafin karatu."




Haka kuma, ofishin jakadancin ya bayyana cewa masu neman gurbin daga Najeriya da Ghana za su iya samun cikakkun bayanai kan shirin da kuma yadda ake neman gurbin ta shafin hukuma na Ireland Fellows Programme.


Tallafin karatun ya haɗa da biyan kuɗin makaranta gaba ɗaya, alawus na kowane wata, tallafin masauki, kuɗin tikitin jirgin sama da na biza, da kuma inshorar lafiya.