Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu, ya bayyana cewa Taʻ ammali da miyagun kwayoyi na da alhakin kusan kashi 80 cikin 100 na matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta, yana mai bayyana matsalar a matsayin babbar barazana ga makomar matasa da ci gaban al’umma.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wani taron lacca da aka shirya domin tunawa da ranar yaki da shan miyagun kwayoyi da safararsu da Majalisar Dinkin Duniya ta ware na shekarar 2026.

Da yake jawabi ta bakin mataimakinsa Alhaji Idris Mohammed Gobir, gwamnan ya ce mafi yawan masu aikata laifukan ta’addanci da garkuwa da mutane suna aikata hakan ne bayan sun sha kwayoyin da ke sa mayen.

Ya ce shan miyagun kwayoyi na lalata rayuwar iyalai, hana matasa cimma burinsu, da kuma kara yawaitar laifuka da matsalolin lafiya da zamantakewa a cikin al’umma.

Gwamna Aliyu ya bukaci matasa su nisanci shaye-shaye domin su samu damar zama shugabanni, ministoci, gwamnoni da manyan jami’an gwamnati a nan gaba, yana mai cewa hakan ba zai yiwu ba idan suka faɗa cikin harkar kwayoyi ko safararsu.