Akwai yiwuwar tawagar matasa ta Rasha ta halarci wata gasa da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) za ta shirya a karon farko tun bayan dakatar da ƙasar daga wasannin ƙasa da ƙasa sakamakon mamayar da ta kai wa Ukraine a shekarar 2022.
FIFA ta bayyana cewa gasar farko ta Kofin Duniya na 'yan ƙasa da shekara 15 (U-15 World Cup), wadda za a gudanar a ƙasar Azerbaijan a watan Oktoba, za ta kasance a buɗe ga dukkan ƙasashen da ke cikin ƙungiyar FIFA.
Tun a watan Fabrairun 2022 ne FIFA ta dakatar da Rasha daga shiga dukkan wasannin ƙasa da ƙasa bayan fara yaƙin Ukraine. Daga baya, sai dai ta sassauta matakin ga tawagogin matasa 'yan ƙasa da shekara 17 na maza da mata.
Duk da hakan, har yanzu Rasha ba ta halarci gasannin U-17 da FIFA da UEFA suka shirya ba, sakamakon ci gaba da kaurace mata da wasu ƙasashen Turai, ciki har da Ukraine da Ingila, saboda yaƙin da ake ci gaba da yi.
Ana sa ran za a fara gasar Kofin Duniya ta 'yan ƙasa da shekara 15 a ranar 22 ga Oktoba, inda za ta gudana na tsawon kwanaki tara a ƙasar Azerbaijan.
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da ko Rasha za ta shiga gasar ba, duk da cewa ƙa'idodin FIFA sun nuna cewa gasar a buɗe take ga dukkan ƙasashen mambobinta.