Fitaccen jarumin masana'antar fina-finan Nollywood, Joseph Momodu, ya shiga rundunar sojin Amurka a hukumance, lamarin da ya nuna sabon babi a rayuwarsa bayan fiye da shekaru goma yana taka rawa a masana'antar shirya fina-finai ta Najeriya.
Momodu ya bayyana cewa ya kammala horaswar soji ta tsawon makonni 10, inda ya ce ya yanke shawarar shiga aikin ne domin girmama marigayi mahaifinsa, wanda ya taba kasancewa jami'i a rundunar 'yan sandan Najeriya.
A cewarsa, ranar da ya shiga aikin, wato 12 ga Afrilu, 2026, ta zo daidai da cikar shekaru 20 da rasuwar mahaifinsa, abin da ya kara ba wannan mataki muhimmanci a gare shi.
Kafin sauya sana'arsa, Joseph Momodu ya yi fice a fina-finai da shirye-shiryen talabijin da dama, ciki har da Coming to Nigeria, Play 2 Kill, A Fool for Trust, Tinsel, Soul Sisters da The Johnsons. Haka kuma ya fito a bidiyon wakar Joromi ta fitacciyar mawakiya Simi.
A shekarun 2018 da 2019, Momodu ya lashe lambar yabo ta Best Body Male a gasar Africa Movie Academy Awards (AMAA), abin da ya kara tabbatar da irin gudunmawar da ya bayar a masana'antar fina-finai ta Afirka.