Ana gudanar da aikin tsaftar muhalli na ƙarshen wata a yau Asabar a jihohi da dama na Arewacin Najeriya, inda gwamnatocin jihohi suka dakatar da zirga-zirgar ababen hawa na wasu sa'o'i domin bai wa al'umma damar gudanar da aikin cikin kwanciyar hankali.
Rahotanni sun nuna cewa hukumomin gwamnati sun fara sa ido tun daga safiyar yau, tare da tura jami'an tsaro da na kula da tsaftar muhalli domin tabbatar da bin ƙa'idojin aikin.
An kuma buƙaci mazauna jihohin su tsaftace gidajensu, unguwanni, hanyoyi, magudanan ruwa da wuraren kasuwanci, tare da zubar da shara a wuraren da aka tanada domin inganta tsaftar muhalli da kare lafiyar jama'a.
Sai dai wasu mazauna yankuna sun yi kira ga gwamnati da ta ƙara wayar da kan jama'a tare da samar da isassun kayan aikin tsafta domin ƙara inganta yadda ake gudanar da aikin tsaftar muhalli a kowane ƙarshen wata.
A wasu jihohi, ciki har da Borno, ana gudanar da aikin tsaftar muhalli ne a Asabar ta farko ta kowane wata, maimakon ƙarshen wata.
Ana gudanar da wannan shiri ne domin rage yaduwar cututtuka, inganta muhalli, da kuma ƙarfafa al'umma su rungumi al'adar tsaftace muhallansu a kai a kai.