Lamarin ya auku ne bayan da ƙasashen Amurka da Iran kowannensu ya ƙaddamar da hare-hare a kan takwaransa, wanda hakan ya zama mafi munin taɓarɓarewar tsaro tun bayan da suka sa hannu kan yarjejeniyar wucin gadi ta zaman lafiya.


Ɓangarorin biyu da ke gaba da ba sa ga macicji sun fito suna zargin juna da laifin keta dokokin yarjejeniyar da aka cimma makonni biyu da suka gabata, wadda aka kulla da nufin kawo ƙarshen rikicin da ya ɗauki tsawon watanni huɗu ana fafatawa.


Gwamnatin Amurka ta ce ta kai hare-hare kan wasu kadarorin dakarun Iran a cikin dare, yayin da ita kuma ƙasar Iran ta mayar da martani a ranar Asabar da cewa ta lalata wasu wurare da ke da alaƙa da dakarun Amurka.




Wannan hari na ranar Asabar da aka kai wa jirgin ɗakon man ya biyo bayan wani makamancinsa da aka kai wa wani jirgin dakon kaya a ranar Alhamis, wanda shi ne ya ruruta wutar wannan sabon rikici.


Masu sharhi sun ce Iran ta sake ƙaddamar da sabon yunƙuri na nuna iko a kan wannan babbar hanya mai mahimmanci a duniya wajen jigilar makamashi, wadda ta soma buɗewa a cikin makonni biyu da suka gabata bayan kwashe watanni tana a rufe.