Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya umarci hukumomin tsaro da su fara bincike nan-take kan kisan shugaban ƙungiyar makiyaya ta MACBAN a jihar, Alhaji Arɗo Risku, tare da abokinsa.
Ya bayyana matuƙar kaɗuwarsa da alhini kan lamarin, yana mai cewa ya zo ne a wani lokaci da jihar ke fara samun zaman lafiya a yankuna daban-daban.
Gwamnan ya ce wannan kisan ba wai kawai abin takaici ba ne, har ma wata ƙoƙari ce ta karya zaman lafiya da sulhun da gwamnatinsa ke ƙoƙarin tabbatarwa, musamman ganin cewa ya faru ne jim-kaɗan bayan wani muhimmin taron tsaro.
Saboda haka, ya buƙaci a gudanar da bincike mai zurfi da gaskiya, tare da kamo waɗanda suka aikata laifin domin gurfanar da su a gaban shari’a
Haka kuma, ya yi kira ga al’umma su kwantar da hankalinsu, yana mai gargaɗin cewa bai kamata a bari masu anfani da rikici su tayar da tarzoma ba, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan