Sabon rahoton Times Higher Education (THE) na shekarar 2026 ya nuna cewa jami'o'i 24 daga Najeriya sun shiga jerin manyan jami'o'in duniya, wanda ya sa ƙasar ta kasance mafi yawan jami'o'i a wannan jerin a nahiyar Afirka.

A cewar rahoton, Jami'ar Ibadan (UI) ce ta kasance ta farko a Najeriya, sai Jami'ar Lagos (UNILAG) a matsayi na biyu, yayin da Jami'ar Bayero Kano (BUK) ta zo ta uku.

Gwamnatin Tarayya ta yaba da wannan ci gaba, tana mai cewa hakan na nuna bunƙasar fannonin koyarwa, bincike da ƙirƙire-ƙirƙire a jami'o'in ƙasar.

Sauran jami'o'in da suka shiga jerin sun haɗa da Covenant University, Landmark University, Ahmadu Bello University (ABU), Federal University of Technology Minna (FUT Minna), University of Ilorin (UNILORIN), University of Jos (UNIJOS), University of Nigeria Nsukka (UNN) da wasu jami'o'in gwamnati da masu zaman kansu.