Dakarun Operation FANSAN YAMMA sun kashe 'yan ta'adda biyu, sun ceto mutum ɗaya da aka yi garkuwa da shi, sun kama mutum takwas da ake zargin masu haɗa kai da 'yan ta'adda ne, sannan sun ƙwato shanu 110 da aka sace a hare-haren da suka kai tsakanin 27 zuwa 28 ga Yuni, 2026 a jihohin Kaduna da Zamfara.
A sanarwar da Kakakin rundunar, Laftanar Kanar Aliyu Danja, ya fitar, ya ce dakarun sun ceto mutum ɗaya da aka yi garkuwa da shi a Giwa, yayin da suka gano gawar wani da 'yan ta'adda suka kashe. Bayan harin da aka kai ƙauyen Dariya, wanda ya yi sanadin mutuwar farar hula ɗaya da jikkatar wasu uku, dakarun sun bi maharan tare da kashe biyu daga cikinsu.
Sanarwar ta ƙara da cewa a Magami da ke jihar Zamfara an kama mutum biyu da ake zargin suna kula da lafiyar yan ta'addan, haka kuma a Polewire da ke Birnin Gwari, dakarun sun kama wasu mutum shida da ake zargin suna taimaka wa 'yan ta'adda bayan musayar wuta da maharan.
A wani samame da aka kai a Ungwan Gora da ke ƙaramar hukumar Chikun, dakarun tare da 'yan sa-kai sun ƙwato shanu 110 da aka sace bayan masu satar shanun sun tsere. Rundunar ta ce za ta ci gaba da kai hare-hare kan 'yan ta'adda, tare da kira ga al'umma su ci gaba da bai wa jami'an tsaro sahihan bayanai.