Shugaban Majalisar Koli da ke kula da harkokin addinin Islama a Nigeria kuma mai Alfarma Sarkin Musulmi Alh Muhammad Sa'ad Abubakar ya bayyana hakan ta hannun Babban Jami'i da ke kula da harkokin al'umma na Majalisar kula da harkokin addinin Islama ta kasa a Nigeria Abbas Jimoh.
Majalisar ta ce al'ummar Musulmai su na sane su ke Kin daukar matakan ramuwa dukkuwa da yadda ake tsokanarsu tare da nuna musu wariya a fannoni daban-daban na samar da ababan more rayuwa.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar ya kuma yi kira da a gaggauta yin adalci akan kashe-kashen da aka yi a jahar Kaduna da Benue tare da gudanar da bincike akan zargin rashin Da'a da wani Jami'in Dan sanda ya nuna.
Hakanan Majalisar Koli da ke kula da Harkokin addinin Islama ta Nigeria ta yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da an hukunta wadanda su ka tafka laifuka a jahohin Kaduna da kuma Benue tare da kira ga al'ummar Musulmai da su cigaba da hakuri tare da kamewa domin ba da dama ga gwamnati da kuma hukumomin tsaro su dauki mataki akai.