Gwamnatin Jihar Kano ta fara aikin gyaran matatar ruwa ta Joda da ke Ƙaramar Hukumar Gabasawa bayan ta shafe shekara bakwai ba ta samar da ruwa.


wannan na cikin sanarwar da Kwamishinan Ruwa na Jihar Kano, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya fitar a ranar Talata 30 ga Yuni, 2026.


Ya ce an gyara rijiyoyi huɗu da ke samar da ruwa, waɗanda suka cika tankunan ajiyar ruwa biyu masu ɗaukar lita 720,000.


Ya ƙara da cewa an gyara ɗaya daga cikin injinan samar da wuta da kuma famfunan tura ruwa biyu, yayin da ake ci gaba da gyaran sauran injinan da famfunan.


Ya kuma bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin ƙara haƙa rijiyoyi da gyara ofisoshin matatar da sauran kayayyakin more rayuwa domin dawo da ita aiki gaba ɗaya, tare da fara samar da ruwa ga al'ummomin da take kula da su nan ba da jimawa ba.