Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta na tara naira tiriliyan 2.5 a matsayin kuɗaɗen shiga na cikin gida a shekarar 2026.
A cewar Hukumar Kula da Ɗa'a a Harkokin Kasafin Kuɗi ta Ƙasa, an ɗauki wannan buri ne bayan bayanan da suka nuna cewa ma'aikatu da hukumomin gwamnati sun samar da kuɗaɗen shiga masu yawa a shekarar da ta gabata.
Hukumar ta ce za ta ƙara sa ido kan kuɗaɗen shiga da rarar kuɗaɗen kamfanonin gwamnati domin inganta tattara kuɗaɗen shiga da ƙarfafa aiwatar da manufofin kasafin kuɗi.