Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa za ta tattauna da gwamnatin Afirka ta Kudu kan batun diyya ga 'yan Najeriya da suka rasa ko suka bar dukiyoyinsu yayin da ake dawo da su gida.
Jami'an gwamnati sun ce ana tattara bayanan kadarorin da mutanen suka bari domin amfani da su a tattaunawar da za a yi tsakanin ƙasashen biyu.
A halin da ake ciki, wani sabon rukuni na 'yan Najeriya da aka kwaso daga Afirka ta Kudu ya isa ƙasar, yayin da gwamnati ke ci gaba da shirin dawo da waɗanda suka yi rajistar komawa gida.
Hukumomi sun ce za su ci gaba da kare muradun 'yan Najeriya tare da bibiyar halin da ake ciki, yayin da suke kira ga 'yan ƙasar da ke zaune a waje da su kiyaye dokokin ƙasashen da suke zaune.