Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa ƙasarsa za ta mayar da martani cikin gaggawa idan aka fuskanci wata barazana ga al'ummarta ko shugabanninta.
Kalaman nasa sun biyo bayan wasu bayanai daga gwamnatin Isra'ila kan yiwuwar ɗaukar matakin soja idan aka samu sabon hari.
Araghchi ya kuma yi kira da a mutunta yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin ɓangarorin, yana mai cewa duk wani kaucewa abin da aka amince da shi na iya ƙara dagula rikicin.
Har yanzu dai ana ci gaba da zaman ɗar-ɗar tsakanin Iran da Isra'ila, yayin da ƙasashen duniya ke kira ga ɓangarorin da su guji matakan da za su ƙara ta'azzara rikicin.