Jami'an tsaro a Afirka ta Kudu sun bayyana cewa an kama kusan mutum 900 bayan zanga-zangar da aka gudanar a sassa daban-daban na ƙasar.
A cewar hukumomi, an kama mafi yawan mutanen ne bisa zargin laifukan da suka haɗa da karya dokokin shige da fice da wasu laifuka, yayin da aka ce yawancin zanga-zangar ta gudana cikin lumana.
Sai dai wasu daga cikin gangamin sun rikide zuwa tashin hankali, lamarin da ya sa aka ƙara matakan tsaro a wasu yankuna.
Shugaban ƙasar, Cyril Ramaphosa, ya ce gwamnati na ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki, tare da kira ga jama'a da su kiyaye doka da oda.