Duk da cewa sauya sheƙar jam'iyya ya zama ruwan dare a siyasar Najeriya, akwai wasu fitattun 'yan siyasa da suka ci gaba da kasancewa a jam'iyyunsu tun bayan dawowar dimokuraɗiyya a 1999. Ga taƙaitaccen tarihin kowannensu:
1. Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya mai ci ya fara siyasa a jam'iyyar Alliance for Democracy (AD), wadda ya taimaka wajen kafawa a 1998. Ya yi gwamnan Jihar Legas daga 1999 zuwa 2007. Daga baya AD ta rikide zuwa AC, ACN, sannan ta haɗe da wasu jam'iyyu suka kafa APC a 2013. Bai taɓa sauya sheƙa zuwa wata jam'iyya ba.
2. Goodluck Jonathan
Jonathan ya shiga PDP tun kafuwarta a 1998. Ya yi mataimakin gwamnan Bayelsa, gwamna, mataimakin shugaban ƙasa, sannan shugaban ƙasa daga 2010 zuwa 2015. Har yanzu bai taɓa barin PDP ba.
3. Kashim Shettima
Tsohon gwamnan Borno kuma mataimakin shugaban ƙasa ya kasance a ANPP kafin jam'iyyar ta haɗe da wasu suka kafa APC. Wannan haɗewa ba a ɗaukarsa a matsayin sauya sheƙa.
4. Nyesom Wike
Wike ya kasance ɗan PDP tun kafuwarta. Ya yi shugaban ƙaramar hukuma, ministan ilimi, gwamnan Rivers, sannan yanzu ministan Abuja. Duk da rikice-rikicen siyasa da ya fuskanta, bai taɓa sauya sheƙa daga PDP ba.
5. Sule Lamido
Ya fara siyasa a PRP, sannan ya shiga PDP a 1998 a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar. Ya yi ministan harkokin waje da gwamnan Jigawa na wa'adi biyu. Har yanzu yana cikin PDP.
6. Ahmed Makarfi
Ya shiga PDP tun 1998. Ya yi gwamnan Kaduna daga 1999 zuwa 2007, sannan sanata kuma shugaban riƙo na PDP. Bai taɓa sauya sheƙa ba.
7. Ibrahim Geidam
Tsohon gwamnan Yobe ya kasance a ANPP kafin haɗewar jam'iyyar zuwa APC. Ya yi gwamna, sanata da kuma ministan harkokin 'yan sanda. Bai taɓa komawa wata jam'iyya ba.
8. Ahmad Sani Yerima
Gwamnan farko na Zamfara bayan 1999 ya yi siyasa a ANPP, sannan ya shiga APC lokacin haɗewar jam'iyyu. Ya ci gaba da kasancewa cikin jam'iyyar ba tare da sauya sheƙa ba.
9. Abdul Ahmed Ningi
Sanata Abdul Ningi ya shiga PDP tun 1998. Ya yi ɗan majalisar wakilai daga 1999 zuwa 2011, sannan sanata daga 2011. Ko bayan ya sha kaye a 2015, bai bar jam'iyyar ba, kafin ya dawo Majalisar Dattawa a 2023.
Waɗannan fitattun 'yan siyasa sun bambanta da yawancin takwarorinsu ta fuskar ci gaba da kasancewa cikin jam'iyyunsu tsawon shekaru. Duk da sauye-sauyen siyasa da aka samu a Najeriya, sun kasance masu biyayya ga jam'iyyunsu, ko kuma suka shiga APC ne kawai lokacin haɗewar jam'iyyu a 2013, ba ta hanyar sauya sheƙa daga wata jam'iyya zuwa wata ba.