Jam'iyyar ADC ta sanar da cewa ta shigar da sunayen Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa da Rotimi Amaechi a matsayin mataimakinsa a tsarin tantance 'yan takara na INEC domin zaɓen 2027.
Jam'iyyar ta ce matakin na daga cikin shirye-shiryenta na tunkarar babban zaɓe, bayan hukumar zaɓe ta buɗe tsarin shigar da sunayen 'yan takara ga jam'iyyun siyasa.
INEC dai ta tanadi wannan tsarin ne domin bai wa jam'iyyu damar miƙa bayanan 'yan takararsu kafin wa'adin da ta gindaya ya cika.