Rahoton "The State of the Health Nation Report 2025" da Ma'aikatar Lafiya da Walwalar Jama'a ta Najeriya ta fitar ya nuna cewa an samu sabbin masu ɗauke da cutar HIV 102,251 a faɗin ƙasar cikin shekarar 2025.

Rahoton ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin da gwamnati da abokan hulɗarta ke yi wajen rage yaɗuwar cutar, har yanzu ana samun ƙarin sabbin masu kamuwa da ita.

A cewar Hukumar NACA, a halin yanzu akwai kusan mutane miliyan 1.9 masu ɗauke da cutar HIV a Najeriya.

Jihohin da suka fi samun sabbin masu HIV a 2025

  1. Lagos – 10,430
  2. Rivers – 6,287
  3. Kano – 6,106
  4. Akwa Ibom – 5,413
  5. Taraba – 4,854
  6. Benue – 4,804
  7. Anambra – 4,468
  8. Kaduna – 3,659
  9. Adamawa – 2,989
  10. Babban Birnin Tarayya (FCT) – 2,764

Wasu Jihohin da Suka Samu Ƙananan Alƙaluma

  • Kebbi – 1,572
  • Katsina – 1,541
  • Yobe – 1,483
  • Enugu – 1,429
  • Kwara – 1,371
  • Osun – 1,093
  • Gombe – 1,083
  • Bayelsa – 982
  • Ekiti – 462

Hukumomin lafiya sun buƙaci al'umma su ci gaba da gwajin HIV, bin hanyoyin kariya, da kuma neman magani cikin gaggawa idan aka tabbatar da kamuwa da cutar, domin rage yaɗuwarta da inganta rayuwar masu ɗauke da ita.