Mataimakin Ministan Harkokin Waje na Iran Kazem Gharibabadi ya ce Tehran za ta yi amfani da wasu kadarorinta da aka daskarar a Qatar wajen siyan kayayyakin bukatun ƙasar, bayan tattaunawar aka kammala a Doha, da ya yi bitar yarjejeniyar fahimtar juna da ta dakatar da yakin da ke tsakanin Iran da Amurka.

Ɗaya daga cikin batutuwa da ke ƙkarkashin yarjejeniyar fahimtar juna da ta dakatar da yakin da ke tsakanin Iran da Amurka, Washington ta amince a saki wasu ƙadarori da kuɗaɗen Iran da aka daskarar a matsayin wani ɓangare na aiwatar da yarjejeniyar.

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Kazem Gharibabadi, ya bayyana haka ne lokacin da yake sanar da kammala tattaunawa a Doha na ƙasar Qatar kan aiwatar da yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma tsakanin Tehran da Washington don kawo karshen yakin Gabas ta Tsakiya.

Masu halartar taron sun amince za'a kafa wani kwamitin sa'ido daga yau Alhamis wanda zai rika tattara bayanai kan duk matakin saɓa ƙa'idodin yarjejeniyar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na IRNA ya ruwaito.

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Qatar ya ce an samu "ci gaba sosai kan batutuwan da suka shafi yarjejeniyar fahimtar junar bayan ganawar da masu shiga tsakani na Qatar da Pakistan suka yi da tawagar Amurka da Iran a Doha.