Bayan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya soke lasisin bankunan microfinance 46, ƴan Najeriya da dama sun fara nuna damuwa kan makomar kuɗaɗensu da ke ajiye a waɗannan bankuna.
CBN ta ce matakin ya biyo bayan gazawar bankunan wajen cika ƙa'idojin da doka ta tanada, ciki har da rashin isassun jari, dakatar da ayyuka ba tare da izini ba, da sauran matsalolin gudanarwa.
Shin kuɗaɗen masu ajiya za su salwanta?
A'a. Bisa dokokin Najeriya, Hukumar Inshorar Kuɗaɗen Ajiya (NDIC) ce ke da alhakin kare masu ajiya idan aka soke lasisin banki.
A cewar masana harkokin banki, NDIC za ta fara tantance bayanan masu ajiya sannan ta mayar musu da kuɗaɗensu gwargwadon abin da doka ta tanada.
Nawa za a biya masu ajiya?
- Idan kuɗin mutum bai wuce naira miliyan 2 ba, za a mayar masa da duka kuɗinsa.
- Idan kuɗin ya wuce naira miliyan 2, za a fara biya shi naira miliyan 2, sannan sauran kuɗin za a ci gaba da biyansa bayan an sayar da kadarorin bankin da aka rufe.
Ta yaya za a karɓi kuɗin?
NDIC za ta yi amfani da lambar BVN domin gano asusun ajiyar mai kuɗi a wani banki, sannan ta tura kuɗin kai tsaye zuwa wannan asusun.
Ga mutanen da ba su da wani asusun banki a wani wuri, za su buƙaci zuwa ofishin NDIC domin tantance bayanansu kafin a biya su.
Hukumomi sun shawarci masu ajiya da su kwantar da hankalinsu, tare da bin sanarwar NDIC domin samun cikakken bayani kan yadda za su karɓi kuɗaɗensu.