Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tabbatar da Sanata David Mark a matsayin halastaccen shugaban jam'iyyar African Democratic Congress (ADC).

Kotun ta yi watsi da ƙarar da ɗan majalisar wakilai, Leke Abejide, ya shigar, tana mai cewa batun shugabancin jam'iyya al'amari ne na cikin gida, kuma mai ƙarar bai gabatar da hujjojin da suka isa ba.

Mai shari'a Musa Liman ya ce sauyin shugabanci daga tsohon shugaban jam'iyyar, Ralph Nwosu, zuwa David Mark ya bi tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam'iyyar, tare da tabbatar da Rauf Aregbesola a matsayin sakataren jam'iyyar na ƙasa.

Kotun ta kuma yanke hukuncin cewa Leke Abejide bai nuna yadda aka take masa haƙƙinsa ba, don haka ba shi da hurumin shigar da ƙarar.

A ƙarshe, kotun ta umarci Abejide ya biya kowanne daga cikin waɗanda ake ƙara Naira miliyan 2 a matsayin diyya, sannan ta umarci lauyansa ya biya Naira miliyan 10 a matsayin kuɗaɗen shari'a.